Senata Mohammed Danjuma Goje (an haife shi a ranar goma 10 ga watan Oktoba, shekara ta alif ɗari tara da hamsin da biyu miladiyya 1952), a Pindiga, Akko,Jihar Gombe an, zabe shi gwamnan Jihar Gombe a shekara ta dubu biyu da uku (2003) karkashin jam'iyar People's Democratic Party (PDP), ya kama aiki daga ranar 29 ga watan Mayun 2003, ya sake cin zaɓe a karo na biyu a shekara ta dubu biyu da bakwai (2007) wanda ya kammala a shekara ta dubu biyu da goma sha ɗaya (2011). A halin yanzu dan jam'iyar All Progressives Congress (APC) kuma sanata mai ci daga Jihar Gombe. A zaɓen watan Afrilun Shekarar dubu biyu da sha ɗaya (2011), Mohammed Danjuma Goje ya nemi takarar zama sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya ƙarƙashin tikitin jam'iyar People's Democratic Party (PDP). Ya karanta kimiyyar Siyasa a Jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya taba zama dan majalisar Jihar Bauchi daga shekara ta alif ɗari tara da saba'in da tara (1979) zuwa shekara ta alif ɗari tara da tamanin da uku (1983). Goje ya rike Sakatare a National Institute For Medical Research dake Yaba Jihar Lagos, daga shekara ta 1984–1989. Ya kafa ta shi kamfanin mai suna, Zaina Nigeria Ltd, a shekarar alif ɗari tara da tamanin da tara (1989) zuwa shekara ta alif dari tara da casa'in da tara (1999). Ya sama kamfanin suna ne daga sunan Mahaifiyarsa, Hajiya Zainab. Danjuma Goje ya nemi takarar kujerar sanata a Nigerian National Assembly a shekarar alif ɗari tara da casa'in da takwas (1998) daga nan ya zama Minister of State, Power and Steel daga shekarar 1999–2001 karkashin Shugaban cin Olusegun Obasanjo..
Developed by StudentB